Isa ga babban shafi

Iran tace duk wanda yace mata kul zata ce cas

Kasar Iran ta yi gargadin cewa muddin aka kai mata hari shakka babu za ta yi fito-na-fito ayi yaki gadan-gadan, ganin yadda kasar Amurka da kawayenta na yankin Gulf ke hararanta da cewa ita ta kitsa kai hari matatun Mai na Saudiya karshen makon daya gabata.

Ministan harkokin wajen Faransa Javad Zarif yayin wani taro a birnin Moscow na kasar Rasha, wanda ya bayyana matakin kasar sa Iran
Ministan harkokin wajen Faransa Javad Zarif yayin wani taro a birnin Moscow na kasar Rasha, wanda ya bayyana matakin kasar sa Iran REUTERS/Evgenia Novozhenina/File Photo
Talla

Mohammed Javad Zarif, Ministan waje na kasar Iran ya shaidawa manema labarai cewa basa kaunar yaki saboda hasarar daka iya biyo baya, amma kuma muddin aka ce dasu kule zasu ce chas, saboda zasu kare kasarsu.

A cewar Ministan ‘yan tawayen Houthi dake Yemen sun amsa cewa su suka kai harin kan Saudiya, amma kuma sai Saudiya da Amurka ke kafewa da cewa Iran ta kai shi.

A halin da ake ciki dai Sakataren waje na Amurka Mike Pompeo, wanda ya zargi Iran, ya bayyana cewa yafi kaunar ganin an warware rikicin kai hare-haren kan cibiyoyin main a Saudiya cikin lumana.

Ya fadawa taron manema labarai bayan ya gana da shugabannin kasar Daular Larabawa cewa yana fatan Iran ita ma ta rungumi sasantawa cikin lumana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.