Isa ga babban shafi

Uwa ko jariri na mutuwa duk dakika 11 wajen haihuwa- rahoto

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna yadda duk Uwa ko Jariri sabuwar haihuwa ke mutuwa duk bayan dakika 11 a sassan duniya, duk da matakan da ake dauka wajen rage yawaitar mace-macen mata yayin haihuwa.

Wata Jaririya da ke fama da matsananciyar rashin lafiya
Wata Jaririya da ke fama da matsananciyar rashin lafiya ©REUTERS/Mohamed al-Sayaghi
Talla

Rahoton wanda WHO ta fitar a yau, ya ci karo da binciken baya-bayan nan da ke nuna nasarar da aka samu a kokarin rage yawaitar mutuwa sanadiyyar haihuwa, inda ya nuna yadda akalla jarirai dubu bakwai ke mutuwa a kowacce rana cikin shekarar bara.

Hukumar lafiyar ta WHO ta ce duk minti 11 jariri guda ko uwa kan mutu sanadiyyar haihuwa ko kuma wata dayan farko bayan haihuwa wanda ke matsayin barazana ga haihuwa 5 da ake samu duk bayan minti guda a sassan duniya.

Shugaban hukumar Lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce ya zama wajibi a dauki matakin magance matsalar mutuwar yara sabbin haihuwa dai dai da nasarar da aka samu ta rage mutuwar kananan yara da shekarunsu basu gaza 5 ba sanadiyyar cutuka gama gari.

A cewar shugaban na WHO jariran da uwayensu sun fi fuskantar kalubale a kasashen da mata masu jiki basa samun cikakkiyar kulawar lafiya, inda ya ce a bara an samu mutuwar kananan yara miliyan 5 da dubu dari 3 ne a duniya baki daya wanda ya nuna raguwar adadin matuka idan aka kwatanta daga shekarun baya.

Rahoton na WHO ya nuna cewa galibin matan da ke mutuwa sanadiyyar haihuwa kan gamu da kalubalen doguwar nakuda ko kuma kulawa da su yadda ya kamata, inda ya ce adadin mata dubu 295 ne suka mutu a bara,ko da dai rahoton ya bayyana yadda aka samu raguwar adadin idan aka kwatanta da shekarar 2000 da mata dubu 451 suka mutu sanadiyyar haihuwa.

Kididdigar WHO ta nuna cewa jumullar mata da jarirai miliyan 2 da dubu dari 8 ke mutwa duk shekara, matakin da shugabar asusun kula da lafiyar kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya Henrietta Fore ke cewa batu ne da ke bukatar kulawar duniya baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.