Isa ga babban shafi
Amurka - Iran

Amurka ta laftawa babban bankin Iran takunkumi

Amurka ta ce za ta tura karin dakarunta zuwa yankin gabas ta tsakiya, sakamakon hare-haren da aka kaiwa filayen hakar man Saudiya, da ake zargin Iran na da hannu a ciki.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Gwamnatin Amurkan ta bayyana matakin ne sa’o’i bayan da shugaba Donald Trump ya bada umarnin kakabawa Iran karin takunkumin karya tattalin arziki, kan wadanda ke kanta a baya, wanda yace shi ne mafi tsauri, da Amurka ta taba laftawa wata kasa.

A wannan karon dai Amurka ta lafta takunkumin karya tattalin arzikin ne kan babban bankin kasar ta Iran, gami da gargadin cewa, takunkumin zai shafi duk wanda ya kulla wata alakar hada-hada da bankin.

A ranar Alhamis Amurka ta yi alkawarin kafa rundunar dakarun hadin gwiwa ta musamman da za ta fuskanci barazanar Iran a yankin gabas ta tsakiya, la’akari da harin da aka kaiwa wasu filayen hakar danyen man Saudiya a ranar 14 ga Satumban da muke ciki.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo ya bayyana haka, yayin ganawa da Yarima mai jiran gadon sarautar hadaddiyar Daular Larabawa a jiya Alhamis.

Tuni dai kasar ta Hadaddiyar daular Larabawa, Saudiya, Birtaniya da kuma Baharain suka bayyana cewa a shirye suke su shiga kawancen kafa rundunar hadakar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.