rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Iran Gabas ta Tsakiya Amurka Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Iran za ta bayyana shirin zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya - Rouhani

media
Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani. AFP/Iranian Presidency/HO

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce zai gabatarwa da majalisar dinkin duniya tsarin tabbatar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, nan da ‘yan kwanaki.


Rouhani ya bayyana haka ne yayin jawabin da ya gabatar yau lahadi a bikin faretin dakarun kasar na shekara.

Shugaban na Iran ya kuma zargi kasashen ketare musamman Amurka da haddasa tarin matsaloli da rikice-rikce a yankin gabas ta tsakiya, da sunan girke dakarunsu da nufin wanzar da zaman lafiya.

Daganta da sake yin tsami tsakanin Iran da Amurka bayan hare-haren da aka kaiwa filayen hakar man Saudiya, wadanda ta zargi Iran da kitsawa.

Ranar asabar, dakarun musamman na Iran suka yi gargadin cewa, duk kasar da ta kuskura ta kai mata hari, za ta dandana kudarta, domin kuwa za su maida ta filin yaki.

Iran ta yi gargadin ne, bayan umarnin da Amurka ta bayar na tura karin dakarunta zuwa yankin gabas at tsakiya, sakamakon hare-haren da aka kaiwa filayen hakar man Saudiya.