rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Isra'ila

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Hadakar Netanyahu da Gantz zai samarwa Isra'ila maslaha-Rivlin

media
Shugaban kasar Isra'ila Reuven Rivlin DR

Shugaban kasar Isra'ila Reuven Rivlin ya bayyana cewar za’a samu gwamnatin da za ta dore a kasar ne kawai idan ta kunshi Firaminista Benjamin Netanyahu na Jam’iyyar Likud da Janar Benny Gantz da ke adawa da shi.


Rivlin ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da wakilan jam’iyyun siyasa domin jin shawarar su kan wanda yafi dacewa ya zama Firaminista saboda kamala zaben makon jiya ba tare da wanda ya samu rinjayen da ake bukata ba.

Kawancen Jam’iyyun da Janar Gantz ke jagoranci sun samu kujeru 33 a Majalisa mai kujeru 120, yayin da kawancen Firaminista Netanyahu ya samu kujeru 31.

Ana saran Rivlin ya bayyana wanda ya dace ya kafa gwamnatin bayan ganawar, sai dai wasu na rade radin cewar yana bukatar Netanyahu da Gantz su kafa gwamnatin hadin kai.