rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Tarayyar Afrika Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

A zuba wa Afrika jari don bunkasa kanta- Buhari

media
Nigerian President, Muhammadu Buhari delivering speech at UN Femi Adeshina/ Facebook

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci kasashen da suka ci gaba da su zuba jari a Afrika domin ganin ta samu ci gaba wajen tsayawa da kafafuwanta, wanda hakan zai magance rikice-rikice da kuma kaura zuwa kasashen duniya.


A yayin da yake gabatar da jawabinsa a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, shugaban ya tabo batutuwa da dama da suka hada da matsalar tsaro da yadda masu tsatsauran ra’ayi ke amfani da kafofin sada zumunta suna aikata laifuka da yaki da cin hanci da rashawa da muhimmancin bada ilimi da kuma tallafa wa marasa karfi.

Shugaban ya bayyana samar da kasar Falasdinu mai cin gashin kanta a matsayin muhimmiyar hanyar warware rikicinta da Isra'ila.