Isa ga babban shafi

Anyi coge wajen zaben Messi a matsayin gwarzon FIFA

Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA, ta fara maida martai kan zargin coge da akayi mata daga sassa daban-daban kan yadda aka gudanar da zaben gwarzon shekara ta FIFA,wanda tace Messi ya lashe.

Dan wasan kasar Masar Mohamed Salah.
Dan wasan kasar Masar Mohamed Salah. Reuters/Andrew Couldridge
Talla

Da take mai da martini ga hukumar kwallon kafar kasar Masar, da ta ce ba’a kirga kuri’un kasarta guda biyu da suka zabi dan wasan kasar Mohammad Salah ba, FIFA ta ce, hakan ya faru ne sakamakon rashin cika ka’idar da masu zaben na Masar sukayi, FIFA tace, kuri’un na Masar guda biyu bai dauke da sahannun sakatare Janar na hukumar kwallon kasar, kana masu jefa kuri’un na Masar sunyi amfani da Manyan harrufa wajen sanya hannu.

Hukumar kwalon kafar Masar dai ta zargi FIFA da kin kidaya kuri’un kasar biyu da kocin kasar Shwky Gharib da kuma Kaftin din Club din Ahmed Elmohamady suka jefawa dan wasan kasar da ke taka leda a kungiyar Liverpool Mohammed Salah, wanda FIFAn tace shi ya zo na 4 a zaben da Messi ya lashe, yayin da Ronalda ya zo na 2, sai Virgil Van Dijk ya zo na 3.

Bayaga hukumar kwallon kafar Masar, akwai wasu da sukayi makaicin wannan korafi.

Kocin kasar Sudan Dravko Lugarisic, yace, shima ya zabi Mohammad Salah, sai kwasam ya gano sunansa cikin wadanda suka zabi Lionnel Messi.

Shi kuwa Kaftin din tawagar kwalon kafar kasar Nicaragua, Juan Barreram, yace kwata-kwata bai shiga zaben ba, amma sai ya kasance cikin wadanda suka zabi Messi a jerin farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.