rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Facebook Twitter

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gwamnatoti da 'yan siyasa na yaudara ta kafofin sadarwar intanet

media
bincike ya nuna yadda gwamnototi da ‘yan siyasa daga kasashen duniya 70, na amfani da kafofin sada zumanta na Intanet wajen yada labaran da ke jirkita hankalin al’umma. Flickr CC / Mike MacKenzie

Wani bincike ya nuna yadda gwamnototi da ‘yan siyasa daga kasashen duniya 70, na amfani da kafofin sada zumanta na Intanet wajen yada labaran da ke jirkita hankalin al’umma.


Cikin wani rahoto da Cibiyar binciken yanar gizo ta Oxford ta fitar ya ce, yaudara ko jirkita labari da gwamnatoti da ‘yan siyasa ke yi, ya ninka cikin shekaru biyu da suka gabata.

Binciken ya gano kafar Facebook ta kasance ja gaba ga masu wannan aiki, bayan da cibiyar ta tattara gamsassun hujjoji daga kasashe 56.

Masu binciken sun ce sun gano jagororin wasu manyan kasashen duniya guda 7, na amfani da Facebook da Twitter sukan zarta iyakokinsu wajen kasalandan ga harkokin kasashen waje.

Rahoton ya bayyana kasashen da China, da Indiya, da Iran, da Pakistan, da Rasha, da Saudiya da kuma Venezuela.

Daraktan Cibiyar mai hedikwata a Burtaniya, Philip Howard, ya ce yaudar al’umma ta kafofin sada zumunta na zama babbar barazana ga dimokiradiyya, inda yace, farfaganda ya zama tamkar rayuwar yau da kullum.