Isa ga babban shafi
Yemen

'Yan tawayen Huthi sun saki Fursunonin 290 a Yemen

‘Yan tawayen Huthi na Yemen sun sanar da sakin Fursunoni 290 ciki har da gommai da suka tsira daga hare-haren hadakar Sojin da Saudiya ke jagoranta, yayin farmakin da ta kai sansaninsu a farkon watan nan.

Wasu 'yan tawayen Huthi na Yemen
Wasu 'yan tawayen Huthi na Yemen ©REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

Matakin sakin Fursunonin na daga cikin wani bangare na yarjejeniyar da ‘yan tawayen suka kulla da gwamnatin Yemen a bara, duk dai a yunkurin warware rikicin kasar.

Tuni dai manyan kungiyoyin agaji na kasa da kasa suka yi maraba da matakin na Huthi inda kungiyar Red Cross ta ce yunkuri ne dai zai kawo nasara a kokarin da ake na sasanta rikicin Yemen

Rahotanni sun bayyana cewa Fursunonin 290 da ‘yan tawayen Houthi suka saki basu kunshi dakarun da ke biyayya ga gwamnatin Yemen da suka kama a watan Agusta ba.

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Yemen Martin Griffiths, wanda ya yi maraba da matakin ya ce fatansu fara dabbaka yarjejeniyar ta 2018 daga bangaren Houthi alamu da ke nuna za a iya nasarar kawo karshen tsare fursunoni da bangarorin biyu ke ci gaba da yi.

Mr Griffiths, ya bukaci bangarorin biyu na ‘yan tawayen Houthi da kuma hadakar Sojin kasashen Larabawa da ke samun goyon bayan Saudiya su ci gaba da girmama yarjejeniyar wajen sakin Fursunonin da ke hannunsu.

Sanarwar sakin Fursunonin da ‘yan tawayen Houthi suka fitar a litinin din nan, sun bayyana cewa sun saki Fursunoni 350 ciki har da ‘yan kasar Saudiya guda 3.

Yanzu haka dai akwai Fursunoni fiye da dubu 2 a hannun ‘yan tawayen na Huthi ciki har da dakarun Sojin Saudiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.