rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
  • Palestinawa 22 hare-hare daga Israela ya kashe a Gaza.
  • Dan kunar bakin wake ya kashe mutun daya a ofishin 'yan sandan Indonesia
  • Yau ake zama a bainin jama'a game da tsige Shugaban Amurka Trump
  • Wasu 'yan kasar Kamaru sun shiga Otel da Shugaba Paul Biya ke ciki a Paris.
  • Tashin Bam a Kabul na Afghanistan ya kashe mutane 7
  • Saudiya, Daular Larabawa da Bahrain za su shiga wasannin kwallon kafa tare

China Hong Kong

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An yi zanga-zangar rage karsashin bikin China

media
Wasu daga cikin masu zanga-zangar rajin mulkin demokradiya a Hong Kong REUTERS/Jorge Silva

Jami’an ‘yan sandan Hong Kong sun harbi daya daga cikin masu zanga-zangar tabbatar da demokradiya a yankin, a daidai lokacin da kasar China ke gudanar da bikin cika shekaru 70 da kafuwar mulkin Kwamunisanci. Masu zanga-zangar sun kudiri aniyar rage karsashin bikin na China wadda suke kallo a matsayin kasar da ke yin katsalandan a yankin na Hong Kong.


A karon farko kenan cikin kusan watanni hudu da jami’an ‘yan sandan Hong Kong suka dirka wa daya daga cikin masu zanga-zangar arsahi, a daidai lokacin da masu boren ke kokarin rage karsashin bikin da China ke yi na murnar cika shekaru 70 da kafuwar mulkin Kwamunisancinta.

A yayin da shugaban China Xi Jinping ke karbar gaisuwar ban-girma daga sojojin kasar kimanin dubu 15 a safiyar yau Talata, masu zanga-zangar a Hong Kong sun dukufa wajen jefe-jefan kwayaye kan zanen hotansa, sannan kuma sun bijire wa umarnin da jami’an ‘yan sanda suka ba su na watsewa.

An kwashe tsawon sa’o’i ana dauki ba dadi tsakanin masu zanga-zangar da jami’an ‘yan sandan a sassa daban daban na Hong Kong, inda wasu daga cikin masu zanga-zangar suka yi ta wurgi da wutar aci-bal-bal da kuma duwatsu.

Sai dai ‘yan sandan sun mayar da martani ta hanyar watsa musu ruwan zafi da hayaki mai sa kwalla har ma da harsashin roba.

Sai dai an samu akasi wajen harbe-harben, domin kuwa daya daga cikin ‘yan sandan ya yi harbin gaske kan wani matashi mai shekaru 18 .

‘Yan sandan sun ce, jami’in ya yi harbin ne domin kare kansa, yayin da matashin ke kan samun kulawa a asibiti.