Isa ga babban shafi
Faransa

Gobara ta gurbata iska da ruwa a Faransa

Al’ummar birnin Rouen da ke Faransa da suka hada da masu rajin kare muhalli na gudanar da zanga-zanga bayan sun bayyana shakkunsu kan bayanan da mahukunta suka yi musu dangane da wata gobara ta ta tashi a wata cibiyar sarrafa sinadarai a makon jiya. mahukunta sun ce, babu wata guba da ta gurbata iska da ruwan da jama’ar yankin ke sha, bayanin da masu zanga-zangar suka ce ba su gamsu da shi ba.

Ana fargabar cewa, gobarar birnin Rouen ya gurbata muhalli da suka hadada iska da ruwan sha.
Ana fargabar cewa, gobarar birnin Rouen ya gurbata muhalli da suka hadada iska da ruwan sha. Thibaut DROUET / AFP
Talla

A ranar Alhamis din makon jiya ne, gobarar ta tashi a cibiyar sarrafa sinadaran na kamfanin Lubrizol mallakin attajirin nan na Amurka wato Warren Buffet, yayin da jami’an kwana-kwana suka kwashe tsawon sa’o’i suna fafutukar kashe gobarar wadda ta rika fitar da wani irin bakin gurbataccen hayki da ya turnuke birnin Rouen da kewayensa.

Bayan aukuwar wannan Ibtila’in ne, jama’ar yankin suka fara shakar wani irin wari mai tayar da hankali, sai dai duk da haka, babban jami’in da ke kula da tsaron yankin Normandy, Pierre Andre Durand ya yi kokarin shawo kan jama’a, inda ya nuna musu cewa, za su iya ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum. Amma dai an  rufe makarantu domin aikin tsaftace su daga gurbatacciyar gubar da gobarar ta yada.

Jami’in ya ce, gwajin da aka gudanar ya nuna cewa, babu wata guba da ta gurbata iska da ruwan sha, amma ya tabbatar da cewa, dattijai masu yawan shekaru na shan wahala wajen shakar numfashi, abin da ya sa aka bukace su da zu zauna a gida.

To sai dai a wani akasi, Ministar Kiwon Lafiyar Faransa, Agnes Buzyn da ta ziyarci yankin, ta ce a zahirin gaskiya, birnin ya gurbace a dalilin gobarar, inda take cewa, ba za ta iya bayar da tabbacin kauce wa fuskantar hatsari ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.