rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Tarayyar Turai Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka za ta lafta harajin biliyoyin Dala kan kasashen Turai

media
Jirgin sama samfurin Airbus na samun tallafi daga kasashen Turai domin gogayya da Boeing na Amurka, lamarin da ya saba wa dokokin kasuwanci na duniya REUTERS/Regis Duvignau/File Photo

Amurka za ta lafta wa kasashen tarayyar Turai harajin Dala biliyan 7.5 sakamakon haramtaccen tallafin kudaden da suke bai wa kamfanin kera jiragen sama samfurin Airbus. Wannan na zuwa ne bayan Hukumar Kasuwanci ta Duniya, WTO ta bai wa Amurkar damar daukar matakin kan kasashen na Turai.


Nan da ranar 18 ga watan Oktoba da muke ciki ne ake sa ran Amurkar ta fara lafta wannan harajin kan kasashen Kungiyar Tarayyar Turai bayan Hukumar Kasuwanci ta Duniya ta yanke hukunci kan haka .

Wannan hukuncin dai shi ne mafi girma da Hukumar Kasuwancin ta yi a tarihinta, wanda ke zuwa a daidai lokacin da ake takun saka tsakanin manyan kamfanonin Airbus da Boeing, abin da ke barazanar tsananta tsamin alakar kasuwanci tsakanin Amurka da kasashen Turai.

Kodayake bayanai na cewa, nan kusa hukumomin Amurka za su fara zaman tattaunawa da mahukuntan Brussels domin lalubo hanyar warware wannan takaddama da ke tsakaninsu, yayin da shugaba Donald Trump ya yaba da hukuncin na Hukumar Kasuwancin Duniyar, yana mai cewa, wata babbar nasara ce ga Amurka.

Shugaba Trump ya kara da cewa, wadannan kasashe na Turai sun dade suna cin dunduniyar Amurka ta fuskar kasuwanci.

Kasashen na Turai sun kwashe shekaru da dama suna bayar da tallafi ga kamfanin na Airbus, lamarin da ya yi illa ga masana’antar kere-keren jiragen sama ta Amurka kamar yadda hukumomin Amurkar suka bayyana.

A zahiri dai, kamata ya yi a kyale kamfanonin na Airbus da Boeing kowa ya ci gashin kansa a kasuwa ba tare da samun wani tallafi ba.