rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Italiya ‘Yan gudun Hijira

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An tsamo gawar 'yan cirani 13 a gab da tsibirin Lampedusa

media
Wani jirgin 'yan cirani Reuters/Guglielmo Mangiapane

Jami’an tsaron gabar teku a Italiya sun tabbatar da tsamo gawar wasu ‘yan cirani 13 ciki har da mata masu ciki 2 bayan kifewar jirginsu mai dauke da mutane 50 gab da tsibirin Lampedusa.


Rahotanni sun bayyana cewa kawo yanzu ana ci gaba da neman gomman ‘yan ciranin ciki har da kananan yara 8 da suka nutse a ruwan.

Da safiyar yau ne jami’an tsaron gabar tekun suka ceto mutane 22 da ransu yayinda su ke ci gaba da laluben wadanda suka bace.