Isa ga babban shafi
China

China ta rusa kaburburan Musulmin Uighur

Kasar China ta rusa makabartun al’ummar Musulmin kabilar Uighur, inda ta tono kasusuwan matattun da aka binne shekaru aru-aru, abin da masu kare hakkin bil’adama suka bayyana da yunkurin shafe duk wata alama da ke nuna wanzuwar wannan kabila a yankin Xinjiang.

Daya daga cikin makabartun al'ummar Musulmin Uighur da ke China
Daya daga cikin makabartun al'ummar Musulmin Uighur da ke China AFP
Talla

Wani bincike da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya gudanar ta hanyar amfani da tauraron dan adam, ya nuna cewa, a cikin shekaru kadai, an rusa gomman makabartun al’ummar a yankin arewa maso yammacin kasar.

‘Yan jaridan AFP sun gane wa idanunsu yadda aka tono kasusuwan matattun, sannan kuma aka watsar da su tamkar shara, yayin da aka shafe kaburburansu ba tare da nuna kulawa ba.

‘Yan kabilar Uighur da ke rayuwa a kasashen ketare, sun ce, wannan rusau din, wani bangare ne na shirin gwamnatin kasar don ganin ta murkushe tsirarun ‘yan kabilar.

Salih Hudayar, daya daga cikin jama’ar Uighur, ya ce, China na son shafe duk wani abu da ke alamta tarihinsu a kasar, yana mai cewa, an rusa kaburburan da aka binne kakannin-kakanninsa.

Gwamnatin China ta tsare akalla Musulman Uighur miliyan guda a sansanin wanke kwakwalwa da ke Xinjiang da zummar yaki da matsalar tsattsauriyar akidar addini, yayin da take ci gaba da sanya idon kwa-kwaf kan ‘yan kabilar da ba a killace su ba.

Kazalika kasar ta haramta wa matan Uighur sanya hijabi kamar yadda ta haramta wa mazansu ajiye dogon gemu.

Kasar China ta ci gaba da yin kunnen kashi duk da caccakar da take sha daga a kasashen duniya kan yadda take azabtar da ‘yan kabilar ta Uighur. Ko a cikin wannan makon, sai da Amurka ta yi barazanar hana Bisar tafiye-tafiye ga hukumomin kasar saboda cin zarafin jama’ar.

A can baya, rahotanni sun ce, an rusa Masallatan da ke ‘yan kabilar ke gudanar da ibadunsu.

Kodayake hukumomin Chinan sun fake kan cewa, ayyukan raya birane ne dalilan da suka sa ta dauki matakinta na rusau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.