rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tattalin Arziki IMF

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rikicin kasuwanci na tarnaki ga tattalin arzaikin duniya

media
Sabuwar shugabar Asusun IMF, Kristalina Gueorguieva. REUTERS/Gonzalo Fuentes

Asusun Lamuni na Duniya IMF, ya ce rigingimun kasuwanci da ke faruwa tsakanin manyan kasashe, na haddasa tarnaki ga hasashen da aka yi na samun ci gaba a fagen tattalin arzikin duniya.


Bayanan na kunshe ne a wani rahoto da asusun ya fitar, a daidai lokacin da rikicin kasuwancin ke ci gaba da tsananta tsakanin manyan kasashe a cewar Kristalina Georgieva wadda ke gabatar da jawabin farko a matsayinta na shugabar asusun na IMF.

Shugabar Asusun na IMF ta ce sa-in-sar da kasashen ke yi a fagen kasuwanci, ta sa habakar tattalin arzikin duniya ta ja baya wanda shi ne makamancinsa a cikin shekaru 10 na baya-bayan nan.

Saboda haka ne IMF ta yanke shawarar sauko da alkalumman hasashe na ci gaba zuwa kasa da sama da kashi 3% a bana, yayin da za a sauko da hasashen shekara mai zuwa da kashi 3 da 5 cikin dari.

A daya bangare kuwa Georgieva, ta yi amfani da wannan dama, domin jaddada kira ga kasashe, domin fara biyan harajin da aka dora wa masana’antu dangane da tururin da suke fitarwa mai gurbata muhalli.

A ranar 15 ga wannan wata na Oktoba ne bankin duniya, zai fitar da nasa alkaluma game da ci gaban tattalin arzikin duniya, yayin da har yanzu ba a kai ga warware rigimar kasuwancin da ake yi tsakanin kasashen Amurka da China ba.