Isa ga babban shafi
Faransa

Taron Lyon ya tara Dala biliyan 14 don yaki da cutuka a duniya

Gwamnatoci da ‘yan kasuwa da masu hannu da shuni daga sassan duniya, sun yi alkawarin bayar da gudunmuwar kudaden da yawansu ya zarta Dala miliyan dubu 14 don yaki da cutar Kanjamau da Zazzabin Cizon Sauro da kuma Tarin-Fuka a duniya.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da Bill Gate a taron yaki da cututtuka a birnin Lyon
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da Bill Gate a taron yaki da cututtuka a birnin Lyon Ludovic MARIN / AFP
Talla

Wannan alkawari ne da aka dauka a karshen taron kasa da kasa kan yaki da wadannan cututuka da ke gudana a birnin Lyon na Faransa.

Tun da farko shugaban Faransa Emmanuel Macron wanda ya jagoranci wannan haduwa ta birnin Lyon, ya ce taron ba zai watse ba sai an tara wadannan kudade.

"Ba zan bari wani ya fice daga wannan zaure ko barin birnin Lyon ba tare da mun tara wadannan kudade Dala milyan dubu 14 ba." in ji Macron.

Macron ya ce, wadannan kudade ba na sadaka ne, mataki ne da aka dauka domin zuba jari wajen yaki da cututtukan.

Ana sa ran kudaden za su taimaka wajen ceton rayukan mutane akalla miliyan 16 daga shekarar 2021 zuwa shekarar 2023.

Shugaban asusun ajiyar kudaden, Peter Sands ya ce, suna sa ran nan da shekarar 2023 su rage yawan mace-macen da Kanjamau da Malaria da Tarin-Fuka ke haddasawa da akalla rabi, kamar yadda suke sa ran kare mutane miliyan 234 daga kamuwa da cututtukan.

Shugaba Macron ya shaida wa mahalarta taron cewa, babban makasudun da suka sanya a gaba, shi ne kawar da wadannan cutuutaka uku daga doran kasa baki daya.

Kasar Amurka ce ke kan gaba wajen bayar da tallafin kudaden, in da ta bayar da zunzurutun Dala biliyan 4.68 kuma tuni Majalsar Dokokin Kasar ta kada kuri’ar amincewa da haka, yayin da a jumulce Faransa ta yi alkawarin bayar da Dala biliyan 1.43.

Kungiyoyin agaji sun yaba da sakamakon taron na Lyon, inda suka bayyana shi a matsayin jin-kai.

Shugaban kungiyar agaji mai yaki da cutar Malaria ta RBM, Abdouraahmane Diallo ya ce, suna kallon wannan taro a matsayin nasara, kuma manuniya ce cewa kan kasashen duniya a hade suke.

Tarin-Fuka da Kanjamau sun kashe mutane kimanin miliyan 1.7 a shekarar 2017, yayin da Malaria ta hallaka sama da mutane dubu 430.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraron kalaman Macron.

01:00

Taron Lyon ya tara Dala biliyan 14 don yaki da cutuka a duniya

Kashi 72% na kudaden da aka tara, za a yi amfani da su ne domin yaki da cututukan a nahiyar Afrika, yankin da ake da dimbin masu fama da cutar Kanjamau da Tarin-Fuka da kuma Zazzabin Cizon Sauro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.