rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mexico

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Karo tsakanin mota da jirgin kasa ya hallaka mutane 8 a Mexico

media
Wasu layinka dogo a kasar Mexico. Daniel Manrique (Roadmaster)/Open access

Mahukuntan kasar Mexico sun tabbatar da mutuwar akalla fasinjojin wata motar safa 8 yayinda wasu 7 kuma suka jikkata bayan taho-mugama da motar ta yi da wani jirgin kasa da ke tsaka da tafiya.


Wasu bayanan hukumar bayar da agajin gaggawa a Mexico ya bayyana cewa Direban motar ya yi kokarin tsallake layin dogon gabanin isowar jirgin a kauyen La Valla na jihar Queretaro amma kuma sai ya kuskure hasashensa.

Wasu hotunan wajen da lamarin ya faru a shafukan hukumar sun nuna yadda jirgin ya nike wani bangare na motar.

Cikin bayanan da hukumar bayar da agajin gaggawar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce tuni aka kwashe mutanen da suka jikkata zuwa sashen bayar da agajin gaggawa na Asibitin birnin.