rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Majalisar Dinkin Duniya Turkiya Syria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Farmakin Turkiya ka iya zama laifukan yaki a Syria- MDD

media
Wasu daga cikin dakarun Syria a yankin arewacin Syria AFP/Delil Souleiman

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da kisan gillar da ake yi wa fararen hula a yakin arewacin Syria, tana mai cewa, hakan ka iya zama laifukan yaki da Turkiya ta aikata a yankin.


Rundunar SDF da Kurdawa ke da rinjaye a cikinta, ta ce, an kashe fararen hula 9 a karshen makon da ya gabata a daidai lokacin da Turkiya ke ci gaba da kai hare-hare a yankin arewacin Syria.

Daga cikin mutanen da aka kashe, har da babbar sakatariyar jam’iyyar Future Syria, wato Hevrin Khalaf mai shekaru 35, wadda mayakan da ke kawance da Turkiya suka finciko ta daga cikin motarta kafin su aikata ta lahira.

Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, jami’anta sun kalli hotunan bidiyon da ke nuna irin kisan da mayakan na kungiyar Ahrar al-Sharqiya mai kawance da Turkiya ke yi wa fararen hular a Syriar.

Hukumar ta ce, hotunan bidiyon da aka yada a shafukan sada zumunta, sun nuna mayakan na Ahrar al-Sharqiya na daukar hoton kansu a daidai lokacin da suka aiwatar a kisan gillar kan Kurdawa akan wata babbar hanyar zirga-zirga.

A halin yanzu dai, Majalisar Dinkin Duniya na kan gudanar da bicnike don tabbatar da sahihancin bidiyon, yayin da ta ce, irin wannan kisan ya saba wa dokokin kasa da kasa, kuma hakan ka iya zama laifukan yaki.

A bangare guda, wani lokaci a yau ne Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai yi zama na musamman domin tattaunawa kan farmakin Turkiya a arewacin Syria.