rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Syria Turkiya Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Turkiya ba ta da niyyar mamaya a Syria- Amurka

media
Sojin Turkiya a Syria REUTERS/Stoyan Nenov

Fadar gwamnatin Amurka ta ce Kasar Turkiya ba ta niyyar mamayar wani yanki a Syria, maimakon haka fatan ta shi ne ganin ta kakkabe barazanar mayakan Kurdawa daga kan iyakarta da Syrian wadanda ta ke kallo a matsayin 'yan ta'adda.


Sanar da fadar ta fitar ta ce Turkiya ta mika mata bukatar ganin ta taimaka mata wajen bata damar kammala fatattakar mayakan Kurdawa daga yankunan da suka mamaye a Syria karkashin yarjejeniyar da suka kulla.

Mai magana da yawun fadar ta Amurka ya tabbatar da cewa ko da wasa Kasar ta Turkiya ba ta da nufin mamayar kowanne yanki a Syria face yunkurin wanzar da zaman lafiya ta hanyar kawar da barazanar Kurdawan.

Kasashen na Turkiya da Amurka dai sun kulla yarjejeniyar da ta bai wa Kurdawan damar ficewa daga yankunansu zuwa tuddan mun tsira cikin kwanaki 5, yarjejeniyar da wa’adinta zai kare a ranar Talata mai zuwa.

Sai dai bangaren Turkiya da mayakan na kurdawa sun zargi junansu tun a sa’o’i kalilan bayan cimma yarjejeniyar da karya ka’idojin da ta kunsa.