rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kamfanonin Magani 4 za su biya diyyar kisan mutum dubu 400

media
Ginin Kamfanin magani na TEVA da ke Isra'ila guda cikin kamfanonin magani 4 da suka amince da biyan diyyar don kaucewa gurfana gaban Kotun Amurka. DRwikipedia

Wasu kamfanoni hudu da ke sarrafawa tare da rarraba magunguna a sassan duniya, sun cimma jituwa da gwamnatin Amurka, domin kaucewa gurfana a gaban kotu, bisa zargin da ake yi masu na yin sanadiyyar mutuwar mutane da dama da kuma yada cutuka.


Karkashin wannan jituwa, kamfanonin hudu wato Cardinal Health, McKesson, AmerisourceBergen da kuma kamfanin Teva da ke Isra’ila, sun amince su zuba dala milyan 260 matakin farko a matsayin diyya domin kaucewa gurfana a gaban kotu.

Wasu larduna biyu da ke jihar Ohio a kasar ta Amurka ne suka shigar da wannna kara, to sai dai ana daf da fara sauraron shari’ar a wannan litinin ne aka cimma jituwa tsakanin bangarorin biyu domin warware rikicin ta ruwan sanyi.

Ana zargin magungunan wadannan kamfanoni ne da cewa sun kashe mutane sama da dubu 400 a cikin shekaru 20 da suka gabata, ko dai saboda rashin ingancin maganin ko kuma rashin bayyana wa masu amfani yadda ya kamata su sha wadannan magunguna.

Da farko dai masu shigar da kara sun bukaci kowane daga cikin wadannan kamfanoni hudu, ya biya bilyoyin daloli a matsayin diyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, yayin da za a yi amfani da sauran kudaden domin kula da mutane da suka samu nakasa ko kuma kamuwa da cututuka saboda shan magungunan.