Isa ga babban shafi
Turkiya

Fiye da mayakan IS 100 sun tsere daga Syria

Wasu rahotanni daga Syria sun bayyana cewa fiye da mayakan IS 100 sun tsere daga kasar tun bayan fara farmakin Turkiya kan mayakan Kurdawa a yankin arewacin kasar.

Wasu mayakan 'yan tawaye a Syria
Wasu mayakan 'yan tawaye a Syria Omar HAJ KADOUR / AFP
Talla

Wani babban jami’in gwamnatin Amurka James Jeffrey da ke tabbatar da batun ya ce babu masaniya kan inda mayakan su ke a yanzu bayan ballewa daga Kurkukun da ake tsare da su.

Jeffrey wanda shi ne shugaban kwamitin kula da al’amuran kasashen ketare na gwamnatin Amurka, ya ce tabbas mayakan da suka tserer da kurkukun sun haura 100.

Matakin dai na da nasaba da fara farmakin Turkiya kan Mayakan Kurdawa wadanda su ke matsayin kan gaba wajen fatattakar mayakan IS ta hanyar taimakon Sojin Amurka, bayan da Amurkan ta dauki aniyar janye dakarunta da ke Syria.

Sai dai Mr Jeffrey ya ce har yanzu Fursunonin na IS da ke tsare a hannun Kurdawa na kulle duk dacewa dai akwai fargabar iya fuskantar ballewarsu kowanne lokaci daga yanzu sanadiyyar yadda Kurdawan ke neman karkatar da yakinsu kan Turkiya maimakon ci gaba da yakar kungiyar ta IS.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.