rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Turkiya Syria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta janye takunkumin da ta kakaba wa Turkiya

media
shugaban Turkiya, Recep Erdogan tare da shugaban Amurka, Donald Trump Murat CETINMUHURDAR / TURKISH PRESIDENTIAL PRESS SERVICE / AFP

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da dage takunkumin karayar tattalin arziki da ya kakaba wa Turkiya, inda kuma ya kare kansa daga daukar matakin janye dakarunsa daga Syria.


Shugaban ya bukaci Hukumar Baitul-malin Amurka da ta cire dukkan takunkumin da aka  malkaya wa Turkiya a ranar 14 ga wannan wata na Oktoba saboda hare-haren da gwamnatin RecepTayyip Erdogan ke kaddamarwa kan mayakan Kurdawa a yankin arewa maso gabashin Syria.

A cewar Trump "wannan takunkumin zamu cire shi, sai idan har an sake samun wata matsalar da ba mu ji dadi ba".

"Na yi magana da jagoran Kurdawa, kuma ya nuna matukar godiya saboda matakin Turkiya na dakatar da hare-harenta". In ji Trump.