rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kwashe mutane dubu 50 saboda gobarar dajin Los Angeles

media
Masu aikin kashe gobara a Los Angeles 路透社。

Akalla mutane dubu 50 aka gaggauta kwashewa daga gidajensu a yankin Arewacin birnin Los Angeles daga yammacin jiya Alhamis zuwa yau Juma’a sakamakon barazanar gobarar dajin da ke ci gaba da mamayar dajin yankin.


Rahotanni sun bayyana cewa, matakin kwashe mutanen ya biyo bayan tsanantar wata kakarfar guguwa da ke kara fantsama wutar dajin ta Los Angeles zuwa sauran sassan birnin da ke gab da dajin.

Acewar ma’aikatar kashe gobara ta Amurka, wutar dajin wadda ta faro a yammacin jiya Alhamis gab da Santa Clarita mai nisan kilomita 65 da arewacin Los Angeles kawo yanzu ta kone kadada dubu 2 da 23.

Ka zalika sanarwar hukumar ta ce gobarar ta kuma kone train gidajen jama’a ko da dai ta ce kawo yanzu babu rahoton rasa rai ko kuma jikkata, inda ake ci gaba da kwashe jama’a don tseratar da rayukansu.

Tuni dai mahukuntan Amurka suka aike da jami’an kashe gobara 500 tare da manyan motocin kashe gobara baya ga jirage masu feshi daga sama don kashe gobarar.