Isa ga babban shafi
Bolivia

Shugaban Bolivia ya bayyana samun nasara duk da sukar kasashe

Gwamnatocin kasashen Amurka Brazil Argentina da kuma Colombia sun bukaci gudanar da zagaye na 2 na zaben Bolivia dai dai lokacin da shugaban kasar mai ci Evo Morales ke ayyana kanshi a matsayin wanda ya lashe zaben da gagarumin rinjaye.

Masu zanga-zangar adawa da ayyana shugaban kasar Bolivia Evo Morales a matsayin wanda ya sake lashe zaben kasar
Masu zanga-zangar adawa da ayyana shugaban kasar Bolivia Evo Morales a matsayin wanda ya sake lashe zaben kasar REUTERS/Manuel Claure NO RESALES
Talla

Cikin sanarwar da hadakar kasashen 4 ta fitar ta nemi gwamnatin kasar ta Bolivia ta kyautata tsarin zabenta tare da kiran zagaye na 2 tsakanin shugaba Morales na jam’iyyar masu ra’ayin ‘yan mazan jiya da kuma Carlos Mesa na Jam’iyyar masu tsaka-tsakin ra’ayi.

Masu sanya idanu kan zaben na Bolivia daga kasashen Arewaci da Amurka sun bayyana shakku kan yiwuwar tabbatauwar adalci a zaben, la’akari da tarin matsaloli suka dabaibaye tsarin kirgen kuri’u bayan kammala zaben.

Bayan ikirarin shugaba Morales game da lashe zaben ne, itama da kanta hukumar zaben kasar ta bayyana a shafinta cewa shugaban ke da nasara dai dai lokacin da aka kirge kashi 99 da digo 8 na kuri’un da aka kada.

Shugaba Evo Morales dai na yunkurin sake darewa kujerar mulkin kasar ta Bolivia ne a karo na 4 sai dai a wannan karon zai iya fuskantar kalubalen daga kasashen yankin Amurka da ke kalubalantar salon kamun ludayinsa.

Yanzu haka dai matakin sanar da sakamakon zaben ya haddasa tarnaki a kasar inda tuni zanga-zanga ta barke a wasu yankuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.