rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Chile Amurka Donald Trump Kungiyar kasashen Asiya Malaysia Rasha Vladimir Putin

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Zanga-zanga ta tilastawa shugaban Chile janye karban bakwanci manyan taruka 2

media
Shugaban kasar Chile Sebastian Pinera yayin jawabi ga 'yan kasar 21 ga watan Oktoban 2019 a birnin Santiago AFP Photos/Chilean Presidency/HO

Kasar Chile ta janye daga karbar bakuncin manyan taruka biyu a Laraban nan, yayin da take kokarin dawo da kasar cikin hayyacin ta bayan zanga – zangar fiye da kwanaki 10 da tayi sanadin mutuwar mutane akalla 20.


Shugaban kasar Sebastian Pinera, ya ce aiki da hankali ne ya yi rinjaye wajen yanke shawarar janyewa daga taron tattalin arziki na kasashen Asiya da yankin Pacific, da kuma taron canjin yanayi na 25.

Kafin wannan janyewar, shugaban Amurka Donald Trump yana shirin yin tozali da Xi Jinping na China don tattaunawa kan batutuwa masu mahimmanci da za su kawo karshen rikicin kasuwanci da ke tsakanin kasashen su yau watanni 18.

Kungiyar kasashen Asiya da yankin Pacific ta bayyana goyon bayan ta da matakin janyewa daga karbar bakuncin wannan taro na tattalin arziki da ya kamata a gudanar a ranakun 16 da 17 ga watan Nuwamba, amma ba ta kawo batun yin taron na wannan shekarar ba sai dai wanda Malaysia za ta karbi bakunci a shekara mai zuwa.

An sa ran shugaba Vladimir Putin na Rasha zai halarci taron canjin yanayin na watan Disamba ita ma matashiyar nan ta kasar Sweden mai rajin kare muhalli, Greta Thunberg tana cikin wakilai dubu 25 da aka gayyata, amma shugaba Pinera ya janye biyo bayan fiye da kwanaki 10 da aka gudanar a kasar.