rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Donald Trump

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dole shugaba Donald Trump ya bayyana shaidar biyan harajin shekaru 8

media
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Leah Millis

Koyun Daukaka Kara a Amurka taki amincewa da bukatar shugaba Donald Trump na kin bayyana takardun biyan harajin shekaru 8 da wata kotu ta bukaci ya gabatar, matakin da ake ganin zai tilasta masa bayyana dukiyar da ya mallaka.


Alkalan kotun guda 3 dake Manhattan sun yi watsi da daukaka karar da Trump yayi, dangane da hukuncin karamar kotun wadda tace shugaban bashi da kariyar kin bayyana takardun harajin.

Alkalan sun bayyana cewar sun yanke hukuncin ne kan shaidun da aka gabatar a gaban su, da kuma matsayin Amurka na cewar babu wanda yafi karfin doka.

Wannan hukunci,wani sabon ci gaba ne a kokarin da ake yi na tsawon shekaru don ganin shugaban ya bayyana kwafin shaidar biyan harajin, kamar yadda ya yi alkawari yayin yakin neman zabe a bainar jama'a, amma sai ya yi shiru da batun.