Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta karrama sojoji Musulmi da suka mutu wajen kare ta

Faransa na bikin tunawa da kawo karshen yakin duniya na farko, wanda aka saba yi a ranakun 11 ga watan Nowamba, inda mahukuntan kasar ke amfani da ranar domin jinjinawa dubban Musulmai Armeniyawa da suka rasa rayukansu wajen ceto kasar ta Faransa.

Jerin mutumin da aka sassaka domin tunawa da sojojin Faransa da suka mutu a kasashen waje, yayin yake-yake daban daban. 11/11/2019.
Jerin mutumin da aka sassaka domin tunawa da sojojin Faransa da suka mutu a kasashen waje, yayin yake-yake daban daban. 11/11/2019. Ministère des armées
Talla

Bikin na bana dai shi ne karo na 101 da kasar ke yi, domin tunawa da ‘yan mazan jiyan da suka kwanta dama.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ne ya jagoranci bikin na bana, inda ya kaddamar da wani mutun-mutumi na farko a harabar Arc de Triomphe na birnin Paris, domin girmamawa ga sojojin Faransa 549 da suka sadaukar da rayuwarsu a yake-yaken da suka yi a kasashen ketare, tun daga shekarar 1963, wato lokacin karshen yakin Algeria.

Cikin dakarun Faransar da ake tunawa da su a yake-yake 17, akwai guda 141 da suka mutu a kasar Lebanon, da 129 a kasar Chadi, da 85 a Afghanistan, da kuma 78 a tsohuwar kasar Yugoslavia.

A ranar Alhamis din da ta gabata, ministan cikin gidan Faransa Christophe Castaner, ya jagoranci wani katsaitaccen buki a babban masallacin birnin Paris, domin girmamawa ga sojoji Armeniyawa Musulmi sama da dubu 100 da suka kwanta dama, domin taimakawa Faransa a yake-yaken da suka nuna bajinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.