Isa ga babban shafi
MDD

Majalisar dinkin duniya, na kokarin mayar da Sauro La'ihi...

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da soma shirin gwajin fasahar takaita haihuwar sauro, shirin da take sa ran zai kawo karshen yaduwar zazzabin Malaria da Zika, da wasu karin cutukan sauron, masu halaka miliyoyin mutane.

a laboratory assistant examining mosquito samples at the Pasteur Institute in the southern Vietnamese city of Nha Trang. Hundreds dead in the Philippines; a threefold increase of cases in Vietnam; hospitals overrun in Malaysia, Myanmar and Cambodia -- deng
a laboratory assistant examining mosquito samples at the Pasteur Institute in the southern Vietnamese city of Nha Trang. Hundreds dead in the Philippines; a threefold increase of cases in Vietnam; hospitals overrun in Malaysia, Myanmar and Cambodia -- deng ©Nhac NGUYEN / AFP
Talla

An dai shafe gwamman shekaru, kwararru na yin amfani da fasahar da ake kira da “Sterile Insect Technique” SIT a turance, wajen takaita haihuwa ko yaduwar kwarin dake lalata amfanin gona, sai dai wannan ne karo na farko da za a gwada wannan dabara wajen yakar nau’ikan sauron da suke yada cutuka ga dan adam.

Daya daga cikin manyan jami’an lafiya a sashin bincike da horaswa kan cutuka na majalisar dinkin duniya, Florence Fouque, tace yanzu haka suna aiki tare da, hukumar bunkasa noma ta duniya da kuma hukumar dake sa ido kan yaduwar makaman nukiliya IAEA, kan shirin takaita haihuwar sauron.

Nau’in sauron da ake shirin soma takaita yaduwarsa kafin afkawa sauran nau’ikan shi ne Aedes albooictus, wanda aka fi yiwa lakabi da damisar yankin asiya, la’akari da yadda sauron ke yada nau’ikan zazzabi da dama ciki har da kwayar cutar zika da zazzabin malaria mai zafi.

Majalisar dinkin duniya ta ce a farkon shekarar 2020 dake tafe za a soma aiwatar da gwajin fasahar takaita haihuwar sauron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.