rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Hong Kong China

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Muna da karfin magance rikicin Hong Kong- China

media
Jami'an tsaro sun yi amfani da ruwan zafi wajen tarwatsa masu zanga-zangar da suka yi dandazo a mashigar wata jami'a. REUTERS

China ta ce, ba za ta kyale zanga-zangar yankin Hong Kong ta rikide zuwa mummunan tashin hankalin da ba za a iya kawo karshensa cikin sauki ba. Jakadan China a Birtaniya, Liu Xiaoming ne ya bayyana haka, inda ya ce suna da iko da kuma karfin kawo karshen boren da al’ummar yankin na Hong Kong ke yi.


Gargadin jakadan na China ya zo ne bayan aikin wucen-gadi na tsaftace titunan yankin Hong Kong daga baraguzan gine-gine da sauran abubuwan da masu bore suka lalata, da wata bataliyar dakarun China ta yi a karshen mako.

Jakadan na China Liu Xiaoming, ya kuma gargadi Birtaniya da Amurka da su kauce wa yin katsalandan a rikicin yankin na Hong Kong.

Yau litinin ‘yan sandan kwantar da tarzoma a Hong Kong suka yi amfani da karfi wajen tarwatsa daruruwan masu zanga-zangar neman komawa tsarin mulkin dimokaradiya da suka mamaye wata Jami’a gami da cinna wa kofar shiga cikinta wuta.

Zanga-zangar da dubban al’ummar Hong Kong suka shafe watanni suna yi, ta samo asali ne daga adawa da kudurin dokar mika masu laifi daga yankin zuwa China domin fuskantar hukunci, sai dai daga bisani boren jama’ar ya tilasta janye ta.