Isa ga babban shafi
Amurka-NATO

Amurka ta caccaki Macron kan NATO

Amurka ta yi kakkausar suka ga kalaman shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron kan kungiyar tsaro ta NATO, ta na mai cewa har yanzu shugaban na kan bakansa na ganin ya nesanta Turai daga NATO.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump Reuters
Talla

Gabanin babban taron NATO cikin makon nan da zai gudana a wajen birnin London na Birtaniya, gwamnatin Trump ta musanta zargin Macron na cewa kungiyar ta NATO na fafutuka ne a yanzu haka sakamakon shakar mutuwa.

A wata ganawar babban jami’in gwamnatin Trump da manema labarai ya bayyana cewa, Macron na son samar da kishiya ga NATO a turai wanda kuma batu ne da bazai samu karbuwar da yake fata ba.

Cikin jawaban Macron na ranar Alhamis din da ta gabata, shugaban na Faransa ya bayyana cewa ya zama wajibi su karkatar da tsamin alakarsu daga kan Rasha da China zuwa ga babbar makiyiyarsu kuma uwa ga ta’addanci.

Tuni dai aka fara fassara kalaman na Macron da wani yunkurin na sake gyatta alakar da ke tsakaninsu da Rasha duk da rawarda ta ke takawa a Ukraine dama mamayar yankin Crimea baya ga goyon bayanta na rabewar gabashin kasar.

Sai dai kuma a jawabin da Donald Trump zai gabatar gaban taron na NATO zai nanata bukatar ganin ani ci gaba da matsa lamba ga kasashen na China da Rasha da ke matsayin babban kalubale ga tsaron duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.