Isa ga babban shafi
NATO

Kasashen NATO 29 na kokarin dinke barakar da ke tsakaninsu

Shugabannin kasashe mambobi a kungiyar tsaro ta NATO, na kokarin dinke barakar da ke tsakaninsu a rana ta biyu ta taron da su ke gudanarwa don murnar cika shekaru 70 da kafuwar kungiyar.

Shugabanni da wakilan kasashe 29 mambobin kungiyar tsaro ta NATO yayin taron kungiyar kan cikarta shekaru 70 da kafuwa da ke gudana a birnin London na Birtaniya.
Shugabanni da wakilan kasashe 29 mambobin kungiyar tsaro ta NATO yayin taron kungiyar kan cikarta shekaru 70 da kafuwa da ke gudana a birnin London na Birtaniya. Yui Mok/Pool via REUTERS
Talla

Duk da sabanin da ke tsakaninsu wanda ya bayyana zahiri kafin fara wannan taro, shugabannin kasashe mambobin kungiyar ta NATO su 29, sun ce a shirye su ke domin tabbatar da tsaron junansu ta kowacce fuska.

Kafin taron wanda ke gudana a birnin London, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana kungiyar ta NATO a matsayin wadda ke daf da mutuwa, kalaman da suka haifar da zazzafen martani daga takwaransa na Amurka Donald Trump da kuma Racep Tayyip Erdogan na Turkiyya.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson mai masaukin baki a taron, duk da cewa yana fuskantar babban kalubale na shirin gudanar da zabe a kasar, to amma ya ce akwai bukatar samun hadin-kai tsakanin kasashen kungiyar ta NATO maimakon rabuwar kawuna.

Domin nuna cewa ba wata baraka a tsakaninsu ne shugabannin kasashen 29 suka rattaba hannu kan wata sanawar hadin-gwiwa a yau laraba, sanarwar da ke jaddada muhimmancin hadin kai da kuma taimakekeniya a tsakaninsu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.