Isa ga babban shafi
NATO

NATO ta tsinci kanta cikin sarkakiya

Sakataren kungiyar NATO Jens Stoltenberg, ya ce kungiyar na fuskantar matsalar tsaro mafi sarkakkiya a tarihin kafuwarta, a daidai lokacin da ake kara samun rabuwar kawuna tsakanin kasashe mambobin kungiyar.

Babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg
Babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg REUTERS/Yves Herman
Talla

Kalaman na Stoltenberg na zuwa ne a daidai lokacin da ake tafka mahawara dangane da yadda taron kungiyar da aka gudanar cikin watan jiya a Birtaniya ya kara fitowa fili da irin rabuwar kawunan da ke tsakanin shugabannin kasashen kungiyar 29.

Sakataren kungiyar wanda ke jawabi ga taron fadada tsaro tsakanin NATO da kasashen yankin gabas ta tsakiya da ya gudana ranar Litinin a kasar Kuwait, ya ce ‘’Abin da muka shaida a birnin London lokacin taron shugabannin, ya kara tabbatar mana da cewa akwai rabuwar kawuna’’.

‘’A tsawon shekaru 15 da suka gabata, kungiyar ba ta taba fuskantar kalubale na tsaro da kuma rabuwar kawuna kamar yadda lamarin yake a yanzu ba’’ a cewar Stoltenberg.

Saboda haka ya ci gaba da cewa ‘’matukar muna son tabbatar da tsaronmu, to ya zama wajibi mu kasance a cikin shiri tare kuma da yin aiki kafa-da-kafa don fuskantar kalubale ta kowane bangare da suka hada da ta sama da ta ruwa da kuma tudu’’, in ji sakataren kungiyar ta NATO.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ne ya fara fitowa fili karara tare bayyana cewa akwai rabuwar kawuna tsakanin kasashe mambobin kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.