Isa ga babban shafi
Iran-Amurka

Fiye da mutane 50 sun mutu a turmutsutsun birne Janar Qasim

Rahotanni daga Iran sun bayyana mutuwar akalla mutane 40 yau talata, yayin turmutsutsun binne gawar Babban kwamandan Sojin Kasar Qasim Soleimani da Amurka ta kashe, yayinda yanzu haka ake da adadin fiye da mutane 200 da suka jikkata.

Dandazon jama'ar da suka halarci birne gawar Janar Qasim Soleimani.
Dandazon jama'ar da suka halarci birne gawar Janar Qasim Soleimani. ATTA KENARE / AFP
Talla

Shugaban sashen bayar da agajin gaggawa na Iran Pirhossein Koolivand ya shaidawa manema labarai cewa fiye da mutane 50 ne suka mutu a turmutsutsun kari kan mutane 213 da yanzu haka ke karbar kulawar gaggawa a Asibiti, yayin jana’izar kammala birne gawar ta Qasim Soleimani a yau Talata.

Yayin kammala birne gawar bayan gudanar da jana’izar kwamandan jiya Litinin a birnin Tehran, ta gudana ne a yankin kudu maso gabashin birnin Kerman mahaifar babban kwamandan Sojin Qasim Soleimani, dubban jama’a ne suka rika hawa kan tsaunuka don samun damar yin bankwanan karshe da Kwamandan, matakin da ya sanya wasu gangarowa yayinda aka rika tattake su.

Sanarwar da asibitin Bahanor da ke tsakiyar birnin na Kerman ya fitar, ya bayyana yadda ya samu gawarwakin mutane 13 baya ga wasu mutane 12 da suka samu muggan raunuka kana wasu 40 da suka samu kananan raunuka.

A juma’ar da ta gabata ne, jiragen Amurka marasa matuka suka farmaki motocin kwamandan na Iran a filin jirgin saman birnin Bagadaza tare da hallaka Janar Qasim Soleimani da ke matsayin babban kwamandan dakarun Iran a Ketare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.