Isa ga babban shafi
Iran

Kasashen duniya sun damu kan nukiliyar Iran

Kungiyar Tarayyar Turai da manyan kassahen duniya na ci gaba da kiraye-kirayen ganin Iran ba ta biye wa Amurka wajen ficewa daga yarjejeniyar nukiliyar da ta cimma da su ba, duk da harin jiragen Amurkan marasa matuka da suka hallaka babban kwamandan Sojin Iran a Bagadaza, a daidai lokacin da Tehran ke ci gaba da juya baya ga ka’idojin da yarjejeniyar ta kunsa.

Shugaban Iran Hassan Rouhani da wasu kwamandojinsa
Shugaban Iran Hassan Rouhani da wasu kwamandojinsa Tasnim News Agency/via REUTERS
Talla

Tun bayan harin na makon jiya da ya kara tsamin alaka tsakanin Iran da Amurka baya ga ‘yan korarsu, Iran ta sha alwashin daukar fansa, yayin da tuni ta fara bijire wa ka’idojin da yarjejeniyar nukiliyarta ta kunsa, ko da dai a hukumance ba ta fito ta bayyanna ficewa daga yarjejeniyar karara ba.

Tuni Iran ta fara gyatta sashen kera makamanta na nukiliya, matakin da ke nuna cewa tana shirin bijire wa waccan yarjejeniya, sai dai Tarayyar Turai ta bakin shugabar kungiyar Ursula von der Leyen ta nemi bangarorin biyu da su sasanta rikicin ta fuskar diflomasiyya maimakon daukar fansa ta fuskar soji.

Yanzu haka dai hadakar Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Turai na shirin wata ganawa ta musamman don tattaunawa kan batun sabon rikicin Iran da ke shirin fadada, bayan kisan gillar Amurkan ga babban hafson sojin Iran Qasem Soleimani.

Ilahirin bangaren Turai, kawayen Iran da na Amurka na cike da fargabar abin da zai je ya zo la’akari da yadda Iran ta ki fayyace ta fuskar da take shirin daukar fansa, ko da dai manyan kasashen na ci gaba da gargadin ta wajen ganin ba ta keta iyaka ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.