rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Amurka Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

A shirye muke mu yi sulhu da Iran-Amurka

media
shugaban Amurka Donald Trump tare da shugaban Iran Hassan Rouhani HO, Nicholas Kamm / AFP / IRANIAN PRESIDENCY

Amurka ta ce a shirye take ta shiga tattaunawar sulhu da Iran ba tare da gindaya wasu sharudda ba bayan tankiyar da ke tsakanin kasashen biyu ta tsananta.


A wata wasika da ta aika wa Majalisar Dinkin Duniya, Amurka ta kare matakinta na kisan kwamandan sojin Iran, Janar Qassem Soleimani, tana mai cewa, ta yi haka ne domin tsaron kanta.

A cikin wasikar, jakadan Amurka a Majaliar Dinkin Duniya, Kelly Craft ya bayyana cewa, Amurka na cikin shirin cimma matsaya da Iran don kauce wa jefa zaman lafiya tsakanin kasa da kasa cikin hatsari.

Wasikar ta kara da cewa, Amurka za ta dauki karin matakai a yankin gabas ta tsakiya domin kare jami’anta da kuma muradunta a yankin.

Sai dai jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Majid Takht Ravanchi ya mayar da martani, yana mai cewa, abin mamaki ne yadda Amurka ke neman zaman sulhu amma take ci gaba da lafta wa Iran takunkuman karayar tattalin arzaiki

Iran ta kai harin ramuwar gayya kan sansanonin sojin Amurka a Iraqi, kuma ta shaida wa Majalisar Dinkin Duniya cewa, ita ma ta yi haka ne saboda kare kanta.

A wannan Alhamis ne ake sa ran Majalisar Wakilan Amurka za ta kada kuri’a kan kudirin tilasta wa shugaba Donald Trump jingine daukar karin matakin soji kan Iran.