rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Sahel Mali Burkina Faso Mauritania Nijar Chadi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Macron na ganawa da shugabannin Sahel kan ta'addanci

media
Emmanuel Macron tare da shugabannin kasashen yankin Sahel REUTERS/Ludovic Marin

Yau Litinin shugabannin kasashen yankin Sahel ke ganawa da takwaransu Emmanuel Macron a garin Pau da ke kudu maso yammacin Faransa don tattauna yadda za a tunkari matsalar ayyukan ta’addanci a yankin Sahel.


Hudu daga cikin shugabannin kasashen na yankin Sahel biyar ne aka tabbatar da cewa za su halarci wannan taro da za a fara a marecen yau, sai kuma wasu manyan baki kamar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, da shugaban Hukumar Tarayyar Afrika Moussa Faki, sai shugaban Majalisar Turai Charles Michel.

Macron ya gayyaci shugabannin kasashen biyar don halartar wannan taro ne a daidai lokacin da ake samun kiraye-kirayen ganin cewa Faransa ta janye dakarunta da yawunsu ya kai dubu 4 da 500 daga yankin na Sahel.

To sai dai duk da kasancewar wadannan sojoji, kusan a kowace safiya ana samun yawaitar hare-hare tare da samun asarar rayukan mutane masu tarin yawa.

Harin baya-bayan nan, shi ne wanda aka kai wa barikin sojin Chinagoder da ke Jamhuriyar Nijar, inda sojoji 89 suka rasa rayukansu.

Ko a ranar Juma’a dubban mutane sun gudanar da tarzomar neman ganin sojojin Faransa sun fice daga kasar Mali.