Isa ga babban shafi
Iraq-Amurka

Makaman roka sun dira kan sansanin sojin Amurka

Makamai masu linzami takwas sun fada kan wani sansanin soji da Amurka ke amfani da shi a cikin kasar Iraki a yammacin ranar Lahadi, a daidai lokacin da ake zaman tankiya tsakanin Amurka da kuma Iran a yankin Gabas ta tsakiya.

Ma'aikatar Tsaron Iraqi ta tabbatar da kaddamar da farmakin kan sansanin sojin na Amurka
Ma'aikatar Tsaron Iraqi ta tabbatar da kaddamar da farmakin kan sansanin sojin na Amurka Reuters
Talla

Ma’aikatar Tsaron Iraki ta bayyana cewa, tabbas makaman masu linzami guda takwas kirar Katyusha sun fada kan sansanin sojin Balad mai tazarar kilomita 80 daga arewacin birnin Bagadaza, to sai dai a lokacin da wadannan makamai suka sauka tuni sojojin Amurka suka janye daga sansanin.

Rundunar sojin Iraki ta ce, dakarun kasar 4 ne suka samu raunuka sakamakon harin, wanda shi ne makamancinsa na 4 da aka kai wa muradun Amurka da ke Iraki daga watan Oktoba.

Babu wata kungiya da ta fito ta dauki nauyin kai farmakin, to sai dai Amurka na danganta shi da kungiyoyi masu goya wa Iran baya da ke da matukar tasiri a cikin kasar ta Iraki.

Tun bayan kashe Janar Qasem Soleimani, Amurka da sauran kasashen da ke cikin gungun kawancen da ke yaki da ayyukan ta’addanci a yankin suka fara sauya wa dakarunsu sansanoni saboda fargabar da ake da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.