Isa ga babban shafi
Iran

Iran na zargin Amurka da tunzura al'ummarta kan jirgin Ukraine

Cikin khudubar sallar juma’a da jagoran juyin-juya halin Iran Ayatollah Ali Khamenei ya gabatar, irinta ta farko cikin shekaru 8, shugaban addinin ya gargadi al’ummar kasar kan yaudarar da Amurka ke shirin yi musu wajen yi musu dadin baki a wani yunkuri na ganin ta tunzurasu sun juya baya ga gwamnatin kasar.

Jagoran juyin juya halin Iran Ayatollah Ali Khamenei.
Jagoran juyin juya halin Iran Ayatollah Ali Khamenei. HO / IRANIAN SUPREME LEADER'S WEBSITE / AFP
Talla

Jagoran juya-juya halin na Iran, Ayatollahi Ali Khamnei, a cikin jawabin khudubar ta sa ta yau gabanin sallar juma’a ya bayyana cewa fitar dangon da al’ummar kasar suka yi wajen jana’izar Babban kwamandan Sojin Iran a Ketare Qasem Soleimani da Amurka ta hallaka makwannin baya, wannan kadai ya isa ya nunawa duniya irin yadda al’ummar kasar ke tare da gwamnati don kuwa da zagon kasan kasashen duniya musamman Amurka.

Cikin khudubar ta Khamnei wadda itace irinta ta farko da jagoran na Shi’a ya gudanar cikin shekaru 8, ya nanata cewa dambarwar kuskuren kakkabo jirgin Ukraine dauke da fasinja 176 bata isa ta shafe batun daukar fansarsu kan Amurka game da kisan Soleimani ba.

A cewar Khamnei, wanda rabonsa da hawa mambarin khudubar juma’a tun a shekarar 2012, ya ce wasu makiya na amfanin da batun kuskuren kakkabo jirgin wajen tunzura al’ummar Iran don su juya baya ga gwamnati tare da hadawa Iran tarnaki ta cikin gida.

Khamenei wanda ya bayyana kuskuren kakkabo jirgin na Ukraine a matsayin babban abin takaici kawo yanzu ya ke ci gaba kuna a zuciyoyin al’ummar kasar da masoyanta, ya manyan makiyan Iran na son siyasantar da lamarin yayinda suke mayar da shi makami keta ga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.