Isa ga babban shafi
Afghanistan

Taliban ta yiwa Amurka tayin yarjejeniyar tsagaita wuta

Kungiyar Taliban ta gabatar wa Amurka da tayin kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita musayar wuta, matakin da ake ganin zai bude kofar maido da tattaunawa tsakanin mayakan da mahukuntan Washington dangane da janye dakarun Amurka daga Afghanistan.

Wasu dakarun sojin Amurka a Afghanistan.
Wasu dakarun sojin Amurka a Afghanistan. AFP/File / THOMAS WATKINS
Talla

Amurka ta kwashe tsawon makwanni tana kira ga mayakan Taliban da su sassauta tashe-tashen hankulan da suka haddasawa, tana mai cewa, hakan ne zai bada damar maido da tattaunwa tsakanin bangarorin biyu a hukumance.

Ana sa ran tattaunawar za ta kai ga cimma yarjejeniyar da za ta sa Amurka fara janye dakarunta daga Afghanistan bayan samun tabbacin maido da zaman lafiya a kasar wadda ta yi fama da rikicin kusan shekaru 20.

Wani babban jami’in Taliban da ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, tayin tsagaita musayar wutar da suka gabatar wa Amurka, na tsawon kwanaki bakwai ne zuwa 10, yana mai cewa, sun yi wannan tayin ne a birnin Doha.

A cewar jami’in, tuni suka kammala kwarya-kwaryar yarjejeniyar tare da mika ta ga wakilan Amurka.

Bangarorin biyu sun kwashe shekara suna fatan cimma yarjejeniya, inda har ya rage kiris su fitar da sanarwa a cikin watan Satumban bara, amma shugaba Donald Trump ya fito ya bayyana wa duniya cewa, yarjejeniyar ta mutu saboda tahe-tashen hankulan Taliban a cewarsa.

Sai dai a cikin watan Disamba ne aka sake farfado da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu a Qatar, amma aka sake dakatar da ita saboda harin da aka kaddamar a kusa da sansanin sojin Bagram da ke karkashin kulawar Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.