Isa ga babban shafi

Adadin attajiran duniya ya rubanya - Oxfam

Kungiyar Agaji ta Oxfam ta fitar da wani sabon rahoto da ke cewa, adadin attajiran duniya ya rubanya a cikin shekaru 10 da suka gabata, yayin da mutane 22 da ke kan gaba wajen arziki suka mallaki kudin da ya zarce abin da matan nahiyar Afrika ke da shi.Wannan na zuwa ne a yayin da shugabannin kasashen duniya ke shirin gudanar da taron tattalin arziki na Davos.

Shugabar Jamus Angela Merkel a taron DAVOS
Shugabar Jamus Angela Merkel a taron DAVOS REUTERS/Arnd Wiegmann/File Photo
Talla

Kungiyar Oxfam ta fitar da rahoton ne da zummar rokon shugabannin kasashen duniya da ke halartar taron tattalin arziki na Davos a duk shekara, da su dauki batun rashin daidaito ta fannin tattalin arziki da muhimmanci.

Shugaban kungiyar ta Oxfam reshen kasar India, Amitabh Behar ya ce, tattalin arzikin duniya na kunshe ne a cikin aljihun wasu attajirai da ‘yan kasuwa, abin da ya sa talakawa ke shakkun wanzuwar ire-iren wadannan attajirai a duniya.

Behar ya kara da cewa, mata da ‘yan mata na cikin dimbin mutanen da ba sa amfana da sabon tsarin tattalin arzikin duniya.

Ana sa ran akalla attajiran duniya 119 da suka mallaki jumullar Dala biliyan 500 su halarci taron na Davos na wannan shekarar kamar yadda kafar Bloomberg ta rawaito, kuma akasarin attajiran sun fito ne daga Amurka da India da kuma Rasha.

Oxfam ta ce, wani karamin gungun attajirai ne ya mallaki tiriliyoyin Daloli kuma akasarinsu maza ne.

Oxfam ta kara da cewa, arzikin da wadannan mutane suka mallaka ya wuce kima, yayin da kuma suke ci gaba da juya tattalin arzikin duniyar a tafin hannunsu duk da karancinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.