Isa ga babban shafi
EU-Isra'ila

EU ta yi watsi da shirin zaman lafiyar gabas ta tsakiya na Trump

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta bayyana rashin amincewar ta da shirin sasanta rikicin Gabas ta Tsakiya da shugaba Donald Trump ya gabatar a makon jiya, inda ta kuma bayyana damuwar ta kan shirin Isra'ila na mamaye karin filayen Falasdinawa.

Babban Jami'in Diflomasiyyar Tarayyar Turai  Josep Borrell.
Babban Jami'in Diflomasiyyar Tarayyar Turai Josep Borrell. Reuters
Talla

Wata sanarwar da Babban jami’in diflomasiyar kungiyar Josep Borrell ya rabawa manema labarai, ta sake jaddada matsayin kungiyar na kafa kasar Falasdinu akan iyakokin ta na shekarar 1967 da kuma shirin musayar filaye wanda bangarorin biyu za su amince a tsakanin su.

Barroll ya ce shirin na Amurka wanda shugaba Donald Trump ya gabatar a makon jiya ya yi karo da matsayin kasashen duniya.

Jami’in ya ce kafin a samu dawamammen zaman lafiya wanda zai dore, ya zama dole bangarorin biyu su tattauna gaba da gaba wajen amincewa da batutuwa da dama da suka hada da iyakokin su da matsayin Birnin kudus da tsaro da kuma 'yan gudun hijira.

Acewar Barroll EU ta damu da shirin mamaye yankunan Jordan da Gabar yamma da Kogin Jordan kuma ta na nazarin zuwa kotu domin hana mamayar da Israila ke shirin yi.

Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Israila, Lior Haiat ya bayyana damuwa kan yadda Barroll ke yiwa Israila barazana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.