Isa ga babban shafi

Kananan yara ba su da kariya lokacin yake yake - Save the Children

Kungiyar  Agaji ta ‘Save the Children’ ta bukaci gwamnatocin kasashen duniya da su tashi tsaye wajen kare kananan yaran da suke fuskantar bala’in yaki da tashe tashen hankula.

Wasu yara a sansanin 'yan gudun hijira a Dffa, Jamhuriyar Nijar.
Wasu yara a sansanin 'yan gudun hijira a Dffa, Jamhuriyar Nijar. AFP
Talla

Rahotan kungiyar yace yara kanana na fuskantar babbar barazana daga yake yake, wajen rasa rayukan su da kuma jikkata su, ganin yadda wasu ke daukar su sojin haya da kuma yadda ake cin zarafin su.

Shugabar kungiyar Inger Ashing tace abin takaici ne ganin yadda duniya ta zuba ido ana cin zarafin yaran ba tare da kaukautawa ba, inda tace daga shekarar 2005 akalla yara 95,000 aka kashe ko aka jikkata, yayin da aka sace dubbai, kana aka hana miliyoyi samun ilimi da kula da lafiya a asibitoci.

Rahotan yace daga cikin ko wadanne yara 6 a duniya, guda na zama a yankin da ake tashin hankali, wadanda suka kai miliyan 415, yayin da hare haren da suke fuskanta suka karu da kashi 170 daga shekarar 2010.

Kungiyar tace yaran Afirka suka fi fuskantar barazanar, inda miliyan 170 daga cikin su ke zama a kasashen da ake yaki, sai kuma Gabas ta Tsakiya inda guda daga cikin yara 3 ke zama a inda ake fama da tashin hankali.

Rahotan ya bayyana kasashen da suka fi fuskantar wadannan matsaloli sun hada da Afghanistan da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da Iraqi da kuma Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.