Isa ga babban shafi
China-Lafiya

Annobar COVID-19 ka iya tafka barna fiye da 'yan ta'adda - WHO

Hukumomin Lafiyar China sun ce an samu karin mutane 121 da annobar murar mashako ta COVID-19 ta halaka a China, kuma 116 daga cikin mamatan sun fito ne daga Lardin Hubei kadai, inda annobar ta samo asali.

Shugaban China Xi Jinping yayin duba aikin cibiyar dakile yaduwar annobar murar COVID-19 dake yankin Anhuali a Beijing babban birnin China.
Shugaban China Xi Jinping yayin duba aikin cibiyar dakile yaduwar annobar murar COVID-19 dake yankin Anhuali a Beijing babban birnin China. Xinhua via REUTERS ATTENTION EDITORS
Talla

Yanzu haka dai annobar cutar ta COVID-19 dake kassara hanyar numfashin dan adam ta halaka jimillar mutane dubu 1 da 488 a kasar ta China.

Kididdigar baya bayan nan da jami’an lafiya a kasar suka fitar kuma ta nuna cewar, mutane dubu 51 da 986 ne suka kamu da murar mashakon ta COVID-19 a Lardin Hubei kadai, tun bayan bullarta a Wuhan babban birnin lardin.

A fadin kasarta China kuwa sabuwar kididdigar ta ce kusan mutane dubu 65 annobar ta shafa, bayan gano karin mutane dubu 5 da 90 da suka kamu.

Kawo yanzu dai annobar murar ta COVID-19 ta bazu zuwa akalla kasashe 25, inda ta halaka mutane 3, a Hong Kong, Philippines da kuma Japan.

A baya bayan nan shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus yayi gargadin cewar, cutar ka iya tafka barna sama da ayyukan ‘yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.