Isa ga babban shafi
Tattalin Arziki

Annobar Covid-19 na barazana ga tattalin arzikin duniya - IMF

Asusun bada lamuni na duniya IMF ya ce annobar murar mashako ta Coronavirus ko COVID-19, ka iya dakile bunkasar tattalin arzikin duniya a shekarar bana.

IMF ta bayyana annobar murar COVID-19 a matsayin barazana ga tattalin arzikin duniya.
IMF ta bayyana annobar murar COVID-19 a matsayin barazana ga tattalin arzikin duniya. AFP
Talla

Shugabar asusun na IMF Kristalina Georgieva, ta bayyana haka ne, yayin jawabi a taron bunkasa ci gaban mata na duniya dake gudana a birnin Dubai.

Kristalina ta ce za a iya tantance karfin barazana ko barnar annobar murar ne ta hanyar la’akari da lokacin da aka yi nasarar kawo karshenta.

A China kuwa adadin wadanda ke kamuwa da cutar murar mashakon ta COVID-19 ya ragu karo na uku a jere.

Sai dai hukumar lafiya ta duniya WHO, tayi gargadin har yanzu ba za a iya hasashen makomar kokarin dakile annobar da ake kan yi ba.

Zuwa yanzu dai annobar murar ta halaka mutane dubu 1 da 665 a China, yayinda wasu dubu 68 suka kamu da cutar.

A Japan kuwa ma’aikatar lafiyar kasar tace adadin mutanen da suka kamu da annobar murar a wani jirgin ruwa data killace fasinjojinsa ya karu zuwa 355.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.