Isa ga babban shafi
China

An samu saukin yaduwar Coronavirus a China

A cikin kwanaki uku a jere, an samu raguwar yaduwar cutar Coronavirus a China, duk da cewa mahukuntar kasar sun bada rahoton sabbin mutane dubu 209 da suka kamu da cutar, sannan 142 suka rasa rayukansu a yau Lahadi.

Al'ummar China na toshe hanci da baki domin kare kai daga kamuwa da cutar Coronavirus
Al'ummar China na toshe hanci da baki domin kare kai daga kamuwa da cutar Coronavirus REUTERS/Johannes P. Christo
Talla

Sai dai wadannan alkaluma sun yi kasa idan aka kwatanta da yadda cutar ta harbi dimbin jama’a tare da lakume rayuka a farko-farkon mako.

A jumulce dai, sama da mutane dubu 68 suka kamu da cutar a China kadai, inda dubu 1 da 665 suka riga mu gidan gaskiya.

Baya ga China, rahotanni sun ce, cutar ta kuma kama kimanin mutane 500 a wasu kasashen duniya kusan 30, yayin da ta kashe mutun hudu a kasashen Faransa da Hong Kong da Philippines da kuma Japan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.