Isa ga babban shafi
Afghanistan

Za a yi zaman lafiyar mako guda a Afghanistan

Nan ba da jimawa ba ne za a shiga yanayi na mako guda babu tashin hankali kamar yadda aka cimma tsakanin Amurka da mayakan Taliban, gabanin yiwuwar sanya hannu a wata yarjejeniyar zaman lafiya.

Ana fatan kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta ta kai ga cimma zaman lafiya mai dorewa a Afghanistan
Ana fatan kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta ta kai ga cimma zaman lafiya mai dorewa a Afghanistan REUTERS/Omar Sobhani
Talla

Kakakin Hukumar Tsaron Afghanistan Javed Faisal ya ce, kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wutar za ta fara aiki ne daga Asabar 22 ga wannan wata na Fabrairu, na tsawon mako guda.

Idan har aka yi nasarar aiwatar da wannan kwarya–kwaryar tsagaita wuta, za ta kasance wani al’amari mai mahimanci a rikicin da aka shafe fiye da shekaru 18 ana gwabzawa a Afghanistan, kana za ta share fagen cimma yarjejniyar da za ta kawo karshen rikicin gaba daya.

Fiye da shekara daya kenan Amurka take tattaunawa da Taliban don cimma yarjejniyar da za ta kai ta ga janye dubban dakarunta, ita kuma Taliban ta yi mata halarcin tabbatar da tsaro a kasar.

Cimma buri a wannan kwaryar-kwaryar tsagaita wuta, zai nuna cewa Taliban ta isa da mayakanta, baya ga nuna halarci gabanin sanya hannu a yarjejniyar zaman lafiya na dindindin, wanda hakan zai kai Amurka ga janye dakarunta sama da dubu 12 da ke Afghanistan.

Jami’an Afghanistan sun ce, ba mamaki a cimma yarjejeniya a ranar 29 ga watan Fabrairun nan a Doha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.