Isa ga babban shafi
Corona-China

Barazanar Corona ta tsananta a Korea ta kudu da Iran da Italy

Kasashen Korea ta kudu Iran da Italy sun sanar da daukar sabbin matakan gaggawa don tunkarar cutar corona ko kuma COVID-19 da kawo yanzu ta hallaka mutane dubu 2 da dari 5 a China inda kuma ta fantsamu zuwa kasashe fiye da 25.

Wasu likitoci da ke kula da masu dauke da cutar corona a China.
Wasu likitoci da ke kula da masu dauke da cutar corona a China. China Daily via REUTERS
Talla

Kasashen 3 sun sanar da hana shige da fice a yankin da cutar ta bulla dai dai lokacin da hukumar lafiya ta duniya WHO ke kokawa da yadda cutar ke gaggawar yaduwa zuwa sassan Duniya.

Can a Italy yanzu haka corona ta hallaka mutane 2 yayinda aka tabbatar da mutane 132 da ke dauke da cutar.

A Iran kuwa kasa ta farko a gabas ta tsakiya da ta samu bullar cutar, yanzu haka ta hallaka mutane 8 yayinda ake da jumullar mutum 43 da suka kamu.

A cewar WHO ta na cike da fargabar wayar gari a samu bullar cutar ta corona a nahiyar Afrika, yankin da ta bayyana a matsayin mai nakasasshen sashen kula da lafiya.

A Korea ta kudu, yayin jawabin kai tsyae da shugaba Moon Jae-in ya gabatar ya ce kasar ta kai kololuwar hadari game da cutar inda yanzu haka ake da adadin mutane 556 da suka kamu da cutar.

Yau Lahadi kadai an samu karuwar mutane 169 da suka kamu a Korea ta kudu inda mutum 3 suka mutu.

Baya ga China yanzu haka Korea ta kudu na cikin ‘yan gaba-gaba a nahiyar Asiya da ke da yawan wadanda suka kamu da cutar kasa da Japan wadda ke da mutane fiye da 600 da ke cikin jirgin ruwan Diamond.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.