rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

EFCC ta fara bincikar jiga jigan PDP a Kano da Sokoto

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta gurfanar da wasu jiga jigan jam’iyyar PDP a jihohin Sokoto da Kano gabanta, bisa zarginsu da almundahanar kudade a lokacin gudanar da zaben shekarar 2015 da ta gabata. A jihar Kano dai hukumar ta sanar da gayyato mutane uku da suka hada da Ambasada Aminu Wali tsohon ministan harkokin wajen Najeriya, da Malam Ibrahim Shekarau tsohon gwamnan jihar, bisa zarginsu da almundahanar kudi naira miliyan 900.