rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Fina-Finai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Hollywood na alhinin rasuwar Gene Wilder

media
Hollywood na ci gaba da bayyana alhinin rasuwar Gene Wilder REUTERS/Shawn Baldwin

Fitattun masu shirin fina finan Hollywood na ci gaba da bayyana alhinin su kan rasuwar Gene Wilder wanda ya rasu jiya yana da shekaru 83.


Mel Brooks ya bayyana Wilder a matsayin gwarzon karni, Rain Pryor ta bayyana shi a matsayin wanda har abada ba za a manta da shi ba.

Wilder ya kwashe shekaru 50 yana shirin fina finai kuma wasu daga cikin wadanda suka yi fice sun hada da ‘Death of a Salesman’ da ‘The Producers’ da ‘Willy Wonka and the Chocolate Factory’.

Sauran sun hada da ‘The Woman in Red’ da kuma ‘The Adventure of Sherlock Holmes ‘Smarter Brother’.