Isa ga babban shafi
Kannywood

''Ba a yiwa Rahama Sadau adalci ba''

Matakin da kungiyar shirya fina-finan hausa ta dauka na dakatar da Rahama Sadau, na ci gaba da haifar da Cece-kuce musamman a Arewacin Najeriya, in da masu ruwa da tsaki a harkar ta fim suka sha bam-bam a ra’ayoyinsu game da hukuncin.

An ta ba dakatar da Rahama Sadau a Kannywood
An ta ba dakatar da Rahama Sadau a Kannywood Rahama Sadau/Twitter
Talla

Bayan wannan matakin da kungiyar shirya fina-finan ta dauka kan jaruma Rahama Sadau saboda samun ta da laifin nuna rashin tarbiya a bidiyon wata waka ta Classiq, har yanzu, Jama’a musamman a kasar hausa na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu, in da wasu suka yi madalla da matakin yayin da wasu kuma suka nuna akasin haka.

Ado Ahmed Gidan Dabino daya daga cikin masu shirya fina-finai a kasar hausa ya ce, yana goyon bayan wannan hukunci domin kasance darasi ga ‘yan baya.

To sai dai wasu daga cikin masu kallon fina-finai na hausa, sun ce ba a yi wa jarumar adalci ba saboda a ganin su, akwai wadanda suka aikata laifin da ya fi nata muni amma ba a ce musu uffan ba.

Masu kallon fina-finai sun ba da misali da Jarumai Irinsu Ali Nuhu da ke taka rawa a fina-finan kudancin kasar da Sani Danja da Adam Zango da suka ce  ya kyautu hukunci ya hau kan su.

Lawan Ahmad daya ne daga cikin jaruman fina-finai na Kannywood da ke bayyana cewa babu laifi a hukunta Rahama Sadau, sai dai ya kamata a sassauta mata hukuncin.

Jaruma Rahama Sadau da ke kasar Indiya a halin yanzu, ta fitar da sakon neman afuwa a bisa kuskuren da aka ce ta aikata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.